ABNA24 : Hukumar ta zargi tashoshin da yada shirye-shiryen bidiyo a kan harbe-harben Lekki, da ake zargin Sojojin Najeriya da aikatawa, daga wasu majiyoyi marasa tushe kamar yadda ministan yada labarai na Najeriya ya fada.
Mukaddashin Babban Darakta-Janar na Hukumar, Farfesa Armstrong Idachaba, shi ne ya sanar da cin tarar a wani taron manema labarai a Abuja, inda ya yi barazanar cewa “ ci gaba da irin wannan halayyar na iya haifar da janye lasisin kafar yada labari.”
Dole ne kafafaen yada labarai su yi aiki yadda ya kamata, wato dole ne su yi aiki da ka’idojin hukumar kamar yadda aka shata su. Ya ce; muna yin tir da bayanai marasa amfani da wasu kafofin sada zumunta suka rika bayarwa, wanda a cewarsa hakan ya haifar da zafin rai, wanda kuma ya kai ga jawo tashin hankali a zanga-zangar lumana da aka fara.
Zanga-Zangar Endsers dai ta haifar da matsaloli a wasu yankuna na Najeriya, musamman manyan biranan kasar da suka hada da Abuja da kuma Lagos, sakamakon yadda zanga-zangar ta rikide ta koma tarzoma, inda jami’an tsaro suka bayyana cewa suna zargin wasu bata gari ne da shiga cikin zanga-zangar, kuma suka sauya mata akala.
342/